Ƴan sanda sun kama wani direban motar haya dake yi wa fasinjoji mata fashi

Rundunar Ƴan sandan jihar Ribas ta ce jami’anta sun kama wani mai suna, Andrew  Nwanna  matukin motar taksi mai shekaru 44 da ake zarginsa da yiwa fasinjojinsa mata fashi.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, Grace Iringe Koko mai magana da yawun rundunar ta ce wanda ake zargin na amfani da mota da wata namba ta musamman a matsayin direban motar haya.

Mai magana da yawun ƴan sandan ta ce rundunar ta samu ƙorafe-ƙorafe da dama akan yadda wanda ake zargin ke kai wa fasinjojinsa mata hari.

“Ya ɗauki wata fasinja mace akan titin stadium a yayin  da suke tafiya sai ya sauya akalar motar ya zuwa tsohuwar GRA inda ya kai mata hari tare da ƙwace mata wayoyinta biyu da ƙarfin tuwo,” a cewar sanarwar.

Har ila yau a ranar 10 ga watan Oktoba Nwanna ya ɗauki wata  mata inda ya yi mata barazana da wuƙa ya ƙwace mata wayoyin hannu aku iPhone 13 da iPhone 15 da kuma Redmi 12.

Iringe ta kara da cewa Nwanna ya kuma kwacewa wata fasinja katin cirar kuɗi na bankin Access, Bible da kuma kuɗi $200.

Ta ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya bayyana wani mai suna Adamu dake sana’ar canji a matsayin wanda ya ke aikata laifin tare da shi.an

More from this stream

Recomended