Jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya dake aiki da caji ofis ɗin ƴan sanda na Iddo dake birnin tarayya Abuja sun kama wani mutum mai suna Nuhu Ezra dake ɗauke da wasu sassan bil-adama.
An kama mutumin ne a ranar 09 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 9 na dare dai-dai lokacin da jami’an suke aiki bisa dogaro da bayanan sirri da suka samu.
An kama shi ne a ƙauyen Gosa Kipikipi dake Lugbe a Abuja yana ɗauke da ƙoƙon kan mutum da kuma wasu sassan jiki.
Da take tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh ta ce “Da aka yiwa mutumin tambayoyi ya ce ya ɗauke su ne a cikin daji lokacin da yake farauta a Kuje kuma ya yi niyar sayar da sassan jikin ne kan kuɗi naira 600,000.”
Tuni dai kwamishinan ƴan sandan birnin, Benneth Igweh ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano ƙashin wane mutum ne, wa aka yi niyar sayarwa da kuma tsawon lokacin da mutumin ya ɗauka yana aikata laifin.