Ƴan sanda sun kama wanda ake zargi da kisan mai sana’ar POS

Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta ce ta kama wani da ake zargi da hannu a kisan Abbas Yuguda wani matashi mai sana’ar POS ɗan shekaru 30 a ƙaramar hukumar Mayo-Belwa ta jihar.

A wata sanarwa ranar Litinin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Sulaiman Nguroje  ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a lokacin da matashin yake dawowa daga aiki.

Mai magana da yawun rundunar ya ce wasu gungun mahara sun farma marigayin inda suka ji masa manyan raunuka a kansa i suka kuma barshi sumamme a cikin jini..

“Bayan samun kiran kai ɗaukin gaggawa jami’ai daga ofishin ƴan sanda na shiya dake Mako-mako sun yi gaggawar isa wurin inda suka yi saurin garzayawa da marigayin asibitin Mayo-Belwa,” a cewar sanarwar..

Sanarwar ta ƙara da cewa likitoci sun tabbatar da mutuwarsa da samun labarin faruwar lamarin ne ya saka mutanen suka harzuƙa inda suka je suka farma wani mai suna Umar SNU ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi da kisan.

More from this stream

Recomended