
Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta ce ta kama mutane huɗu da ake zargi da ƙona wata mata ƙurmus har lahira a yankin Abagana dake jihar.
A wata sanarwa ranar Lahadi, mai magana da yawun rundunar, Tochukwu Ikenga ya ce ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi da aikata laifin mace ce mai shekaru 21 da aka bayyana da suna Chinenye Ekwenugo ƴar ƙaramar hukumar Danukofia ta jihar.
Ikenga ya ce Ekwunugo ta amsa cewa ita da sauran mutanen da ake zargi da kuma saurayinta wanda ya tsere su ne suka aikata haka.
Mai magana da yawun rundunar ya ce ƴan sanda sun gano gawar matar, keken guragu da kuma akwatin gawa.
Ya ƙara da cewa rundunar na cigaba da ƙoƙarin kamo sauran wanda ake zargi kuma tuni aka kai gawar matar dakin ajiye gawarwaki.