Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami’an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi da makami, haɗa baki da aikata laifi da kuma kisan kai.

A wata sanarwa, Buhari Abdullahi mai magana da yawun rundunar ya ce kamen  wani ɓangare ne na rage yawan aikata laifuka a jihar.

Abdullahi ya ce waɗanda aka kama sun haɗa da Ahmad Shu’aibu mai shekaru 24, Abubakar Usman mai shekaru 24 da kuma Nuhu Jibrin mai shekaru 30.

Ɗaya daga cikin abokan aikata laifin na su ya tsere ana nemansa ruwa-a-jallo.A

Sulaiman Isa mazaunin unguwar Tudun Wada Pantami shi ne ya kai ƙorafin cewa gungun wasu mutane sun shiga gidansa ɗauke da adduna,wuƙaƙe da kuma sanduna inda suka ya masa barazana.

Waɗanda da ake zargin sun ɗauke masa babur ƙirar Heojue UD, wayoyin hannu guda 6, gwala-gwalai, bandir ɗin kuɗi da kuma dutsen guga.

Bayan ƙorafin ne jami’an ƴan sanda daga ofishin ƴan sanda na Low Cost suka kama Jibrin har ta kai ga kuma kama Shuaibu da Usman tare da gano wasu daga cikin kayayyakin.

Waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannun a fashi da makami, satar motoci da wasu Laifuka kuma an taɓa kama su a baya.

Za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

Har ila yau rundunar ta kama Abdulwahab Abubakar mai shekaru 16 da Sadiq Abdullah mai shekaru 15 da aka zargin su da farwa Sanusi Jibrin tare da ƙwace masa waya akan titin Riyal Bye-pass.

Waɗanda ake zargin sun yi amfani da adda inda su ka jiwa Jibrin ciwo ta hanyar saran sa a  kai.

Abdullahi ya ƙara da cewa ƴan sandan sun kuma kama Haruna Ibrahim mai shekaru 20 da ake zargi da kashe Auwalu Maigadali dake ƙauyen Takulma a ƙaramar hukumar Akko ta jihar.

More News

Magoya bayan jam’iyar NNPP sun ƙona jar hula

Wasu daga cikin mambobin wani tsagi na jam'iyar NNPP sun barranta kansu da jagoran jam'iyar na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso inda suka riƙa...

Magoya bayan jam’iyar NNPP sun ƙona jar hula

Wasu daga cikin mambobin wani tsagi na jam'iyar NNPP sun barranta kansu da jagoran jam'iyar na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso inda suka riƙa...

PDP ta ɗauki hanyar warware rikicin jam’iyar

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya ce  an kawo karshen rikicin cikin gida da ya dabaibaye jami'yar PDP. Mohammed wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin...

Dakarun Najeriya sun cafke wasu ƴan’aiken ƴanbindiga a Kaduna

Sojoji sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da kaiwa 'yan bindiga sakonninsu a kasuwar ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia a...