Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce ta kama mutane huɗu da aka samu da sace kayayyakin tallafi da aka bawa mutanen da ambaliyar ta shafa a jihar.
Mutanen da suka faɗa hannun rundunar sun haɗa da Abubakar Usman, mai shekaru 32, Mohammed Bukar,mai shekaru 37, Ibrahim Abubakar, mai shekaru 28, da kuma Jamilu Mohammed, mai shekaru 24.
Ambaliyar ruwan da ta faru a ranar 10 ga watan Satumba ta raba dubban mutane da gidajensu musamman a yankunan Fori, Galtimari, Gwange, da kuma Bulabulin dake Maiduguri.
Bayan ambaliyar ruwan gwamnatin jihar Borno ta karɓi tallafi daga dai-dai kun mutane, hukumomi, kamfanoni, gwamnatocin jihohi da gwamnatin tarayya.
Da yake magana a wurin wani taron manema labarai ranar Alhamis,Daso Nahum mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Borno ya ce waɗanda ake zargin sun sace kayan tallafin daga wata cibiyar raba kayan dake makarantar Firamaren Babagana Wakil Memorial dake Maiduguri.
A cewar Nahum kayan da aka sace sun hada da buhun shinkafa 5 mai nauyin 25kg, barguna guda shida,katan ɗin makaroni biyu, tabarmi shida sai kuma gidan sauro guda uku.
Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu kuma nan bada jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu.