Ƴan sanda sun kama masu sayen kuri’a a zaben gwamnan Edo

Jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya sun kama wasu mutane 9 da ake zarginsu da sayen kuri’a da kuma mallakar kuri’ar da aka riga aka dangwala.

A wata sanarwa ranar Asabar, Muyiwa Adejobi mai magana da yawun rundunar ya ce mutane 6 da ake zargi an kama su ne a makarantar sakandaren Aibotse dake kusa da otal ɗin Meremu a garin Auchi inda ake zarginsu da sayen kuri’a.

Adejobi ya ce mutanen da ake zargin an same su da kuɗaɗe masu yawa, tarin makamai da kuma bayanai kan yadda suka tsara tayarwa da masu kada kuri’a hankali.

Har ila yau rundunar ta samu nasarar kama wani ɗan jarida na bogi dake tare da mutanen.

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...