Ƴan sanda sun kama masu safarar bindiga a jihar Kaduna

Jami’an ƴan sandan kwantar da tarzoma dake aiki da Sikwadiran na 47 dake Zariya a jihar Kaduna sun samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da safarar bindigogi.

Mutanen biyu sun faɗa hannun jami’an tsaron ne lokacin da jami’an suke gudanar da aikin sintiri akan hanyar Jos zuwa Zaria.

Hukumomin ƴan sandan jihar sun ce jami’an tsaron sun yi amfani da bayanan sirri da suka samu kan ƙoƙarin safafar makamai a jihar abun da ya kai ga kama mutanen biyu.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna,ASP Mansur Hassan a wata sanarwa da ya fitar ya ce waɗanda aka kama sun haɗa da Zubairu Musa mai shekaru 40 da kuma Nasiru Sa’idu mai shekaru 17 dukkansu ƴan asalin ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

ASP Hassan ya ce an kama mutanen da wata  jaka dake ɗauke da bindigogi ƙirar gida manya guda 8 da kuma ƙarama ɗaya sai kuma harsashi guda 6.

More from this stream

Recomended