Ƴan Sanda Sun Gayyaci El-Rufai Da Wasu Jiha-jigan ADC Kan  Zarge-Zarge Tayar Da Tarzoma

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, tare da wasu manyan jami’an jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) guda bakwai domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da suka shafi cin hanci na hadin baki, tayar da tarzoma, barna da kuma jikkata mutane.

Wata wasikar gayyata da aka sanya wa hannu ranar 4 ga Satumba, 2025, ta Mataimakin Kwamishinan ƴan sanda da ke kula da sashin binciken manyan laifuka (CID), Uzainu Abdullahi, ta umarci shugaban ADC na jihar ya kawo El-Rufai da sauran mutanen zuwa ofishin sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID) a ranar 8 ga Satumba.

Cikin jerin sunayen da aka gayyata akwai Bashir Sa’idu, Jafaru Sani, Ubaidullah Mohammed (wanda aka fi sani da 30), Nasiru Maikano, Aminu Abita da kuma Ahmed Rufa’i Hussaini (wanda aka fi sani da Mikiya).

A cewar wasikar, mai taken “Investigation Activities: Case of Criminal Conspiracy, Inciting Disturbance of Public Peace, Mischief and Causing Grievous Hurt”, gayyatar na da nufin bai wa waɗannan mutane damar fayyace zarge-zargen da aka kai kansu.

A wani lamari daban, jami’an tsaro sun rufe ofishin jam’iyyar ADC da ke lamba 4, titin Ali Akilu, Kaduna, a ranar Laraba, awanni kaɗan kafin shugabannin jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma su kai ziyara domin jajantawa ƴan jam’iyyar da suka jikkata a harin da wasu ƴan daba suka kai wa taron hadin gwiwa tsakanin jam’iyyun SDP da ADC a makon da ya gabata.

Shaidu sun bayyana cewa an girke motocin sintirin ƴan sanda da dama a kusa da ofishin, lamarin da ya toshe hanyar shiga wurin jam’iyyar adawar.

More from this stream

Recomended