Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta ce jami’anta sun samu nasarar ceto wata mata daga wani da ake zargin ɗan fashi da makami ne ko kuma matsafi.
A wata sanarwa mai magana da yawun rundunar ƴan sandan birnin, Josephine Adeh ta ce an ceto matar ne ranar Juma’a a wani otal dake Wuse.
Adeh ta ce matar mai suna, Promise Eze ƴar shekara shekara 25 daga jihar Ebonyi an gano ta bata cikin hayyacinta bayan da aka ɗaureta a cikin ɗakin otal inda ake zargin wani da suka gamu a intanet da aikata mata haka.
” A ranar 31 ga watan Janairu 2025 da misalin ƙarfe 11:30 na rana rundunar ta samu kiran kai ɗaukin gaggawa daga wani Otal a Wuse inda su ka ce suna jin motsin da basu yarda da shi ba a cikin ɗaya daga cikin dakuna su,”
Da isar jami’an tsaron sun same ta a daure a kujera kuma bakinta a rufe inda suka garzaya da ita asibiti.
Binciken da jami’an suka gudanar ya nuna cewa wani mai suna Emmanuel Okoro wanda ya tsere shi ne ya aikata haka bayan da ya tsere da wayoyin hannunta guda biyu.