Ƴan sanda sun ceto wani ɗan ƙasar Isra’ila da aka yi garkuwa da shi a Taraba

Rundunar ƴan sandan jihar Taraba da haɗin gwiwar dakarun sojoji da kuma mafarauta sun ceto wani injiniya ɗan ƙasar Isra’ila, Gil Itamar daga hannun masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Takum ta jihar Taraba a ranar Alhamis.

Da safiyar ranar Alhamis ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da Itamar a garin Atim dake kan hanyar Takum zuwa Chanchangi.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP  James Lashen ya ce ƴan sanda sun samu labarin garkuwa ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe ba tare da bata lokaci ba suka  kaddamar da aikin kubutar da shi tare da taimako sojoji a yankin Takum.

Itamar na aiki ne da wani kamfani mai suna SCC dake garin na Takum.

More from this stream

Recomended