Ƴan sanda sun ƙwace jabun ƙuɗaɗe na naira biliyan 129

Rundunar Ƴan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun ƙwace jabun kuɗaɗe da darajar su ta kai naira biliyan  ₦129.

A wata sanarwa ranar Talata, Muyiwa Adejobi mai magana da yawun rundunar ya ce mutane uku  a ka kama da ake zarginsu da mallakar kuɗaɗen na jabu.

Adejobi ya bayyana sunayen, Nura Ibrahim, Muhammad Muntari da Usman Abdullahi a matsayin waɗanda ake zargi.

“Ba jimawa a Kano ƴan sanda sun yi nasarar gano kuɗin naira biliyan N129,542,823,000 na kuɗin  jabu da suka haɗa da jabun dalar Amurka ta miliyan 3,366,000, kuɗin CFA 51970 da kuma miliyan 1,443,000 na kuɗin naira,” ya ce.

Sanarwar ta ce an samu gagarumar nasarar kama mutanen ne a ranar 8 ga watan Disamba a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar.

More from this stream

Recomended