
Mutane 7 ciki har da wata matar aure ƴan fashin daji suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai da daddare a garin Kontagora hedkwatar ƙaramar hukumar Kontagora ta jihar Neja.
Mazauna garin sun faɗawa jaridar Daily Trust cewa anyi garkuwar ne ranar Lahadi da daddare a wasu gidaje dake wajen garin.
Unguwannin da abun ya shafa sun haɗa da Talba Estate, Rafin Karma, Dadin Kowa, Gangaren-Sagi, da kuma Kontagora bypass.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa a cikin mutanen da aka yi garkuwa da su har da wata mata da mijinta ya samu nasarar tserewa daga ƴan fashin dajin.
Wani mazaunin yankin da yaki bayyana sunansa ya koka kan yadda ƴan bindiga suke yawan kawo hari a yankin.