Ƴan fashin daji sun sace kusan mutane 61 a ƙauyen Buda dake ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan fashin dajin sun kai hari kan kauyen ne da tsakar daren ranar Litinin.
Dauda Kajuru wani mazaunin ƙauyen ya ce ƴan fashin dajin sun zo garin ne su da yawan gaske inda suka riƙar harbin kan me uwa da wabi.
Ya ce wasu daga cikin danginsa wanda abun ya rutsa da su inda ya ƙara da cewa martanin gaggawa da dakarun sojoji suka yi shi ya hana ƴan bindigar tafiya da mutane masu yawan gaske.
“Abin da ya faru jiya abun na da firgici sosai ƴan fashin dajin sun zo da niyar sace mutane da yawa fiye da ɗaliban makarantar da suka sace a Kuriga ta ƙaramar hukumar Chikun amma saurin ɗaukin da sojoji suka kawo waɗanda sansani s bai fi kilomita biyu ba daga Kajuru shi ya sa yawan mutanen ya ragu,”
Shima Lawan Abdullahi wanda mazaunin ƙauyen ne da ya tsira daga harin ya bayyana cewa matarsa da ƴaƴansa da kuma wasu mata biyu ciki har jariri ɗan sati biyu na daga cikin waɗanda aka sace.