
Ƴan fashin daji dake ɗauke da makamai sun kashe ƴan bijilante shida a jihar Kebbi.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi ya ce an kashe su ne a harin kwanton da aka kai musu a ranar Juma’a lokacin da suke bin sawun ƴan fashin dajin da suka saci shanu a ƙauyukan Dantulu da Rusakde dake ƙaramar hukumar Arewa ta jihar.
Ƴan fashin dajin sun kai farmaki ƙauyukan a ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da dabbobi abun da ya sa ƴan bijilante suka bi sawun su.
Amma kuma sai suka yi wa ƴan bijilanten kwanton ɓauna washe garin ranar da daddare a dajin Matankari inda suka kashe su.
Dakarun rundunar sojan Najeriya, ƴan sanda da kuma sauran ƴan bijilante su ne suka sami gawar ta su.