Wasu da ake zargin ƴan fashin daji ne sun kai farmaki mazaɓar Kakangi dake ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka kashe ƴan bijilante huɗu da kuma ɗan sandan kwantar da tarzoma guda ɗaya
Ƴan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutanen da basu san adadinsu ba a kusa da wata gona dake yankin Sabon Layi duka a mazaɓar.
Yahaya Musa Dan Salio mamba mai wakiltar al’ummar mazaɓar Kutemeshi a majalisar dokokin jihar Kaduna ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin a ranar Litinin.
Ya ce ” Eh a cikin waɗanda abin ya shafa akwai ƴan bijilante da kuma wani mutum guda da ƴan fashin dajin suka kashe a ranar Lahadi. Akwai kuma wasu mazauna ƙauyen da aka yi garkuwa da su a gonakinsu dake wajen Sabon Layi dukkansu a ƙarƙashin mazaɓa ta.”
Shima mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan ya tabbatar da kisan mutanen.