Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama wasu mutum uku da ake zargi da sace wani matashi, inda suka harbe shi a ƙafa bayan sun gano cewa ba shi da isasshen kuɗi a asusun bankinsa.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Bright Edafe, ya bayyana cewa wanda ake zargin sun karɓi Naira miliyan biyu daga asusun wanda suka sace, amma duk da haka suka harbe shi don “koyar da shi darasi.”
Edafe ya ce lamarin ya faru ne a garin Ogwashi-Uku, inda aka samu kiran gaggawa cewa an sace wani matashi daga gidansa. Rundunar ta yi amfani da fasahar bin diddigin waya har ta gano inda masu laifin ke ɓoye a cikin daji a yankin Ogwashi-Uku, inda aka ceto wanda aka sace da raunin harbin ƙafa.
Ya ce binciken da aka gudanar ya kai ga kama Chukwuebuka Nka da Uche Okechukwu a jihar Anambra, inda aka gano motar wanda aka sace — Toyota Venza farar launi.
Bayan amincewar waɗanda aka kama, jami’an tsaro suka kai samame a wani kauye mai suna Agidiase da ke Ogwashi-Uku, inda suka kama wanda ake zargin na uku, mai suna Somto Chukwuma.
Rundunar ta kuma gano motar da suke amfani da ita wajen aikata laifuka da wata na’urar katse sadarwa (network jammer) a maboyarsu.
DSP Edafe ya tabbatar da cewa bincike na ci gaba, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.
Ƴan Fashi Sun Harbi Wanda Suka Sace Bayan Sun Gano Ba Shi Da Isasshen Kuɗi a Asusun Bankinsa
