Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta ce jami’anta sun kama wasu mutane uku da ake zarginsu da aikata fashi da makami a jihar.
Tochukwu Ikenga mai magana da yawun rundunar ya ce jami’an rundunar sun kuma gano wata motar sata daga hannun mutanen.
Ikenga ya ce an kama mutanen da ake zargi ne a cikin wata mota baƙa ƙirar LEXUS 330 ranar Laraba a mahadar Kwata dake Awka babban birnin jihar.
Mutanen da aka kama sun haɗa da Ifesinachi Okonwko mai shekaru 22, Chisom Okafor mai shekaru 20 da kuma Oderah Ebenezer mai shekaru 20 a lokacin da ake musu tambayoyi sun amsa cewa sun sato motar daga ƙauyen Isuaniocha.
Sanarwar ta ce waɗanda aka kama na daga cikin masu aikata laifin da suka addabi mutane a jihar har ila yau rundunar ta yi kira da duk wanda aka kwacewa mota ƙirar Lexus da ya garzaya hedkwatar rundunar.