Godwin Abumusi shugaban kungiyar ƴan fansho ta Najeriya ya yi barazanar jagorantar ƴan ƙungiyar domin yin zanga-zanga tsirara matukar ba a inganta walwalarsu ba.
Da yake magana da ƴan jaridu a Abuja ranar Asabar,Abumusi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kayyade naira dubu 100,000 a matsayin mafi ƙarancin kuɗin fansho da za a rika biyan ma’aikacin da yayi ritaya.
Shugaban ƙungiyar ya yi gargadin cewa duk abin da za ayi da ya gaza buƙatar da suka miƙa wa gwamnati to zai jawo mambobin kungiyar su gudanar zanga-zanga tsirara akan tituna.
“A Najeriya gwamnati bata damu da talaka ba kansu kawai suka sani idan ba haka ba ta yaya ɗan fansho a jihar Enugu zai riƙa karbar N450 duk wata ta yaya haka zai faru,” a cewar Abumusi.
Ya ce suna son su gabatar da buƙatar biyan Naira 100,000 ga kwamitin da aka kafa da zai sake duba mafi ƙarancin albashi kamar yadda ƙungiyar kwadago ta gabatar da naira dubu 200,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.