
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama ƴan daba da dama a wani samame da jami’an rundunar su ka kai wasu unguwanni dake cikin ƙwaryar birnin Kano.
An kama ƴan daban ne biyo bayan kwanaki da aka kwashe suna gwanza a faɗa a unguwannin Kofar Mata, safe da Zango.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta bayyana cewa rundunar ta samu wannan nasara ne biyo bayan ziyarar gani da ido da kwamshinan ƴan sandan jihar, Salman Dogo Garba ya kai wuraren da aka yi faɗan daba ya kuma bayar da umarnin ɗaukar matakin gaggawa.
Mutane 24 aka kama tsakanin ranakun 13- 16 ga watan Disamba a samamen da aka kai unguwannin.
Kwamishinan ƴan sandan ya godewa al’ummar jihar kan goyon baya da su ke bawa rundunar.