
Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ɗalibai huɗu a jihar Katsina.
Ƴan bindigar sun farma rukunin gidaje na unguwar Paris dake bayan Jami’ar Tarayya ta Dutsinma da misalin ƙarfe 02:20 na daren ranar Lahadi.
Wasu majiyoyi dake garin sun bayyana cewa maharan masu yawan gaske sun farma garin inda suka yi awon gaba da mutane huɗu.
Mutanen da aka yi garkuwa da su sun haɗa da Wali Kayode, Fahad Emmanuel da kuma wani da ba a san sunansa ba.
Jami’an tsaro sun yi gaggawar isa wurin biyo bayan kiran kai ɗaukin gaggawa da aka yi musu amma tuni maharan sun tsere kafin su isa wurin.
Wata majiyar jami’an tsaro ta bayyana cewa ana cigaba da ƙoƙarin bin sawun masu garkuwandomin ceto mutanen.