Ƴan bindiga sun sace wasu ɗaliban jami’a biyu a Taraba

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai biyu na Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Wukari a jihar Taraba.

A cewar rahotanni ƴan bindigar sun farma wani ɗakin kwanan ɗalibai dake wajen jami’ar akan hanyar Wukari  zuwa Zaki Biam inda suka sace ɗaliban mace da namiji.

Mai magana da yawun jami’ar, Misis Adore Auwudu  ta ce tuni aka sanar da jami’an tsaro kuma suna bin sawun masu garkuwa ya zuwa cikin daji.

Idan za a iya tunawa shugaban jami’ar ta Wukari, Farfesa Jude Sammani Rabo a wurin wani taron manema labarai gabanin bikin yaye ɗaliban jami’ar ya yi ƙorafin cewa rashin wadataccen wurin kwanan ɗalibai a cikin jami’ar na jefa rayuwar dalibai cikin hatsari.

More from this stream

Recomended