Ana zaman ɗarɗar a Masarautar Zuru a Jihar Kebbi bayan ’yan bindiga sun kutsa Government Girls Comprehensive Senior Secondary School, Maga, a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu. Harin ya yi sanadin mutuwar Mataimakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, sannan ’yan bindigar sun yi awon gaba da wasu dalibai.
Wata mazauniyar yankin, Murjanatu Hassan Gishiri, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana cewa ’yan bindigar sun shigo makarantar ba tare da wata turjiya ba. Ta bayyana cewa harin ya jefa jama’a cikin tsananin firgici.
Har yanzu ba a bayyana adadin daliban da aka sace ba, domin hukumomi ba su fitar da cikakken bayani ba.
Hukumomin tsaro ba su fitar da sanarwa kan lamarin ba tukuna.
Ƴan Bindiga Sun Sace Dalibai A Kebbi Tare Da Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta

