Ƴan bindiga sun kashe wani matashi akan hanyarsa ta zuwa ɗaurin auren ɗanuwansa a Zamfara

Ƴan fashin daji sun kashe wani matashi a wani hari da suka kai musu akan hanyar Tsafe dake jihar Zamfara.

Matashin  mai suna Haruna Bello Muhammad Karmanje ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da su ke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan uwansa Ibrahim Bello Karmanje a garin na Tsafe.

Ƴan bindigar sun buɗe wuta kan motar da su ke ci lokacin da su ke tsaka da tafiya.

Danuwan marigayin Imam Sani shi ne ya sanar da rasuwar a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Jihar Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin yankin arewa maso  yamma dake fama da yawan hare-hare daga ƴan bindiga.

Kawo yanzu rundunar ƴan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan faruwar harin.

More from this stream

Recomended