Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sum kashe fasto Tobias Chukwujekwu Okonkwno na Cocin Katolika Gundumar Nnnewi a jihar Anambra.
A wata sanarwa ranar Juma’a shugaban cocin, Raphael Ezeogu ya ce ƴan bindigar sun kashe marigayin ne ranar Alhamis a garin Ihiala dake kan titin Onitsha zuwa Owerri.
” Ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba ne su ka harbe shi a Ihiala dake kan babbar hanyar Onitsha zuwa Owerri wajen karfe 7 zuwa 8 na dare,” a cewar sanarwar.
Kisan faston na ƙara haska yadda ake cigaba da samun ƙaruwar kashe-kashe da aikata sauran laifuka musamman a yankin na kudu maso gabashin Najeriya.
A ranar Talata ma wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da Justice Azuka mamba a majalisar dokokin jihar Anambra lokacin da yake tafiya akan titin Ugwunapampa a yankin Onitsha.
A ranar 7 ga watan Disamba ma an sanar da ɓacewar Godwin Okpala limamin Cocin Anglika a jihar ta Anambra.