Wasu ƴan bindiga sun kashe Shagari Ebije’ego mai girma Onu na Itama basaraken gargajiya dake ƙaramar hukumar Dekina a gidansa dake garin.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun bi sawun basaraken gargajiyar har gida da yammacin ranar Litinin inda suka harbe shi har lahira.
Mazauna garin sun ce wasu ƴan bindiga sun shiga garin inda suka zarce kai tsaye zuwa gidan marigayin.
“An ga makasan nasa su da yawa a cikin abun hawa ɗauke da makamai sun nufi gidan basaraken dake garin da misalin ƙarfe 09:00 na daren ranar Litinin,”
“Ba jimawa kaɗan muka fara jin harbi daga wajen gidan abun da ya sa mutane suka sa mutane kowa ya yi takansa.”
Kafin rasuwar tasa marigayin shi ne basarake mafi ƙarancin shekaru a ƙaramar hukumar ta Dekina.