
Ya bindiga sun kaddamar da farmaki a yankin Heipang dake ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato da safiyar ranar Laraba inda suka kashe shanu da dama tare da jikkata Wasu.
A cewar, Ibrahim Babayo shugaban ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyettti Allah ƴan bindigar sun yi dirar mikiya a yankin inda suka riƙa harbin kan me uwa da wabi abun da ya tilastawa masu kiwon arcewa tare da barin shanunsu.
Ya ce an kashe shanun ne lokacin da suke kiwo a yankin ya ƙara da cewa haka kawai aka kai farmaki.
Shugaban ya ce tuni su kai rahoton faruwar lamarin ga jami’an rundunar Operation Safe Haven dake aikin samar da tsaro a jihar.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaron sun basu tabbacin cewa za su binciki lamarin.