Ƴan bindiga sun kashe mutum guda tare da sace wasu da dama a jihar Neja

Ƴan bindiga sun kai farmaki wasu ƙauyuka dake ƙananan hukumomin Munya da Shiroro a jihar Neja inda suka kashe mutum guda ɗaya tare da sace shanu da ba a san adadinsu ba.

A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro an kai harin na Shiroro ne a ranar 22 ga watan Fabrairu da misalin ƙarfe 02:15 na rana inda ƴan bindiga dake kan babura suka farma ƙauyukan Kutako Makera da Galadiman Kogo.

Makama ya ce maharan sun harbe wani mai suna Bansi Kutako mai shekaru 75 kafin suyi garkuwa da mutanen ƙauyen da dama da sace shanunsu.

A wani harin na daban ƴan bindigar sun kai farmaki ƙauyen Hayin Dogo dake ƙaramar hukumar Munya da misalin ƙarfe 03:50 na daren ranar 23 ga watan Fabrairu inda suka sace mutanen ƙauyen biyar ciki har da mata biyu.

Waɗanda aka yi garkuwa da su sun haɗa da Adamu Danfulani, Umar Sanda, Murtala Tela, Aisha Rabiu, da kuma Ramatu Murtala mai shekaru 23.

A cewar Makama tuni tawagar jami’an tsaro da ta ƙunshi DSS, sojoji, ƴan sanda da kuma mafarauta suka fara bin diddigi maharan domin ceto mutane da kuma shanu da aka sace.

More from this stream

Recomended