Shugaban Karamar Hukumar Bukkuyum da ke Jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Umar-Faru, ya bayyana cewa akalla mutane 1,065 ne aka kashe a yankin tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu sakamakon hare-haren ’yan bindiga.
Umar-Faru ya ce rashin tsaro ya tilasta wa jama’a kaura daga gidajensu tare da kawo cikas ga noma da sauran harkokin tattalin arziki. Ya kara da cewa dukkan gundumomi 17 na karamar hukumar sun fuskanci hare-hare, lamarin da ya sa mazauna yankin ke biyan kudin fansa domin rayuwa.
A cewarsa, an biya sama da naira biliyan 2.9 a matsayin kudin fansa da haraji da aka tilasta wa al’umma, yayin da ’yan bindiga suka kwashe shanu 84,928, awaki 52,423 da raƙuma 187.
Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa sama da mutane 200, ciki har da mata da yara, na nan a hannun masu garkuwa da mutane, tare da kiran Gwamnatin Tarayya da ta kaddamar da gagarumin farmaki domin kawo karshen matsalar tsaro a yankin.
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 1,065 A Bukkuyum Tun 2015 – Shugaban Karamar Hukuma

