Ƴan bindiga sun kashe mutane 9 a jihar Filato

Rundunar ƴan sandan jihar Filato ta ce mutane 9 aka kashe a ƙauyukan Zurak da Dakai dake ƙaramar hukumar Wase ta jihar Filato a ranar Litinin.

Ƴan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Zurak da misalin ƙarfe biyar na ranar inda suka kashe wasu mutane da dama.

Wasu mazauna ƙauyen sun ce saboda rashin ingancin sabis na waya a yankin basu samu sun kai rahoton faruwar lamarin ba.

Shafi’i Sambo wani shugaban matasa a yankin ya ce maharan sun isa ƙauyen akan babura ɗauke da muggan makamai.

Ya ce  sun riƙa harbin kan me uwa da wabi.

A wata sanarwa ranar Laraba, Alfred Alabo mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Filato ya ce ƴan bindigar sun fuskanci turjiya mai ƙarfi daga jami’an tsaro.

Ya ce ƴan bindigar sun samu nasarar ƙona gidaje shida.

“An kashe wasu daga cikin ƴan bindigar a yayin da aka kama ɗaya a Dajin Bangalala a ƙaramar hukumar ta Wase da yayi iyaka da jihohin Bauchi,Taraba da Filato.”ya ce.

More from this stream

Recomended