Ƴan bindiga sun kashe mutane 7 a wata kasuwa a jihar Yobe

Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan fashin daji ne sun kashe aƙalla mutane  bakwai  wadanda yawancinsu ƴan kasuwa ne tare da jikkata wasu 11 a kasuwar shanu ta Ngalda da kuma babbar kasuwar garin dake ƙaramar hukumar Fika ta jihar Yobe.

Waɗanda ake zargin ƴan fashin daji ne sun yi dirar mikiya a kasuwar dake ci mako-mako da misalin ƙarfe 6 na yamma inda suka riƙa harbin kan me uwa da wabi tare da yi wa mutane fashi.

Dauda Yakubu Damazai dake taimakawa shugaban ƙaramar hukumar Fika kan harkokin soshiyal midiya ya faɗawa jaridar Daily Trust cewa ƴan kasuwa 7 aka kashe a babbar kasuwar garin da kuma kasuwar shanu.

“jiya (Litinin) da maraice ƴan bindiga sun kai hari kasuwar shanu ta Ngalda da kuma babbar kasuwa mutane bakwai da basu ji basu gani ba maharan suka kashe,” ya ce.

“Aƙalla mutane bakwai ne suka jikkata aka garzaya da su babban asibitin Fika. Mun gode Allah da aka kashe uku daga ciki ƴan fashin.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya ce wasu gungun ƴan bindiga ƙarƙashin jagorancin Alhaji Dadji Ngalda su ne suka kai harin.

Ya ce ƴan fashin sun samu nasarar yin awon gaba da kuɗin da yawansu ya kai miliyan 16 a yayin da mutanen garin suka samu nasarar kashe uku daga ciki tare da kama Alhaji Dadji.

More from this stream

Recomended