Ƴan bindiga sun kashe mutane 13 a jihar Niger

Ƴan bindiga sun kashe mutane 13 a lokacin da suke aiki a gonarsu dake Anguwan Mai-Giro a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Niger.

Harin da ya yi sanadiyar kisan manoman an kai shi ne a ranar Laraba.

A wata sanarwa mataimakin gwamnan jihar Niger  Yakubu Garba ya bayyana harin a matsayin shaidanci da kuma tsabagen rashin tausayi.

Ya ce akwai abun damuwa sosai a ce mutum ne yake aikata haka ga ɗan uwansa mutum.

Mataimakin gwamnan ya nuna alhininsa tare da miƙa saƙon ta’aziyarsa ga iyalan da suka rasa ƴan uwansu dama al’ummar Shiroro baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar zata cigaba da dagewa a ƙokarin da take na dawo da zaman lafiya a faɗin jihar.

More from this stream

Recomended