
Rundunar ƴan sandan jihar Anambra, ta ce jami’an tsaro bakwai ƴan bindiga su ka kashe a yankin Ihiala dake jihar.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Tochukwu Ikenga ya faɗawa ƴan jaridu cewa an kai harin ne da tsakar daren ranar Litinin abun da ya jefa ruɗani da fargaba a zukatan mutanen yankin.
Ikenga ya ƙara da cewa Nnaghe Itam kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar da umarnin gaggauta farauto ƴan bindigar.
“Kwamishinan ya miƙa saƙon ta‘aziyarsa ga iyalan da suka rasa ƴan uwansu a harin da ya kashe jami’an tsaro 7 da kuma wasu mutane biyu dake kan hanya,” a cewar mai magana da yawun rundunar ƴan sandan.
Ya da ƙara cewa jami’an tsaron haɗin gwiwa sun samu nasarar ceto ɗaya daga cikin mutanen da abun ya rutsa da su wanda a yanzu haka yake samun kulawar likitoci a asibiti.
Ikenga ya cigaba da cewa Itam ya ziyarci wurin da lamarin ya faru inda ya tattauna da wasu shedun gani da ido.