Ƴan bindiga sun kai hari ofishin ƴan sanda a Borno

Jami’an ƴan sanda a jihar Borno sun daƙile wani hari da ƴan bindiga su ka kai ofishin ƴan sanda na Jakana dake jihar

A wata sanarwa ranar Lahadi, Muyiwa Adejobi mai magana da yawun rundunar Ƴan Sandan Najeriya ya ce wasu mutane ne da ba a san ko su waye ba su ka kai harin da misalin ƙarfe 11 na dare.

Adejobi ya ce maharan sun jikkata jami’in ɗan sanda ɗaya a harin.

“A cikin sa’a maharan sun gamu da turjiya daga zaratan dakarun rundunar Ƴan Sandan Najeriya  wanda suka samu nasarar daƙile harin tare da jiwa maharan raunuka iri-iri na harsashi a yayin da jami’in guda ɗaya ya jikkata inda yake asibiti yana karɓar magani,” a cewar sanarwar.

A wani labarin na daban Adejobi ya bayyana cewa jami’an ƴan sanda da haɗin gwiwar jami’an tsaro  sun kai farmaki guraren da ake aikata laifi da kuma sansanonin masu garkuwa da mutane a jihar Sokoto a ranar 25 ga watan Nuwamba .

Ya ce jami’an tsaron sun gano bindigar AK-47 gidan zuba harsashi dake cike harsashi 30.

More from this stream

Recomended