Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane Biyu A Wani Hari A Kauyen Daron Da Ke Jihar Filato

Wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a kauyen Daron da ke cikin yankin Gyel na Karamar Hukumar Jos ta Kudu, Jihar Filato, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wani mutum guda.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:50 na yammacin ranar Talata.

Shugaban matasan ƙauyen kuma shugaban ƙungiyar Berom Youths Moulders Association, Solomon Dalyop, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.

Dalyop ya ƙara da cewa harin ya biyo bayan wani gargaɗi da aka samu cewa za a kai hari kan wasu ƙauyuka a yankin Gyel da makwabtansu.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Filato, Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Rahotanni sun ruwaito cewa wannan hari ya ƙara jaddada matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan Jihar Filato, inda al’ummomi da dama ke fama da tashe-tashen hankula.

Gwamnan jihar, Caleb Mutfwang, ya sha nanata cewa gwamnatinsa tare da hukumomin tsaro suna aiki kafaɗa da kafaɗa domin kawo ƙarshen waɗannan ayyukan ta’addanci, tare da kira ga masu aikata hakan su daina tashin hankali su rungumi zaman lafiya.

More from this stream

Recomended