Ƴan Achaba Sun Yi Zanga-Zanga a Bauchi Kan Kwace Baburansu

An samu cikas ga harkokin kasuwanci da na yau da kullum a garin Bauchi ranar Talata, sakamakon zanga-zangar da masu babura na haya (Achaba) suka gudanar kan abinda suka bayyana a matsayin cin zarafi daga jami’an kula da zirga-zirga na VIO.

Masu baburan sun koka kan yadda ake yawan kwace musu babura saboda rashin lambar rijista, ko kuma saboda babu “body number” da lasisin tuki. Sun ce wannan mataki yana jefa su cikin mawuyacin hali ta fuskar samun abin dogaro da rayuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa daruruwan masu baburan sun fito kan manyan hanyoyin garin Bauchi suna tuka babura tare da rera taken koke-kokensu, suna kuma neman a daina musu irin wannan tsauraran matakai.

Wannan zanga-zanga ta haddasa cinkoso a wurare da dama, inda aka ga direbobin sun taru a bakin kofar shiga garin Bauchi. Haka kuma sun toshe tituna a kan hanyar Bauchi–Jos, Yandoka Road, Ahmadu Bello Way da Yakubun Bauchi Road, lamarin da ya tilasta wa direbobi da fasinjoji tsayawa cak.

Wasu daga cikin masu baburan sun bayyana cewa sana’ar su ce kadai hanyar samun abinci da kula da iyalansu, suna masu gargadin cewa tsauraran matakan kwace babura na kara jefa su cikin matsanancin halin rayuwa.

Jami’an tsaro sun kasance a wuraren domin tabbatar da cewa lamarin bai rikide ya zama tashin hankali ba, kuma babu rahoton tashin hankali da aka samu a yayin zanga-zangar.

A halin yanzu, gwamnatin jihar Bauchi da hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba game da wannan al’amari.

More from this stream

Recomended