Ƴan ƙwadago sun janye yajin aiki a Najeriya

Mambobin kungiyar kwadagon da suka hada da Nigeria Labour Congress da Trade Union Congress, a ranar Talata, sun dakatar da yajin aikin na kwanaki biyar, kamar yadda wani jigo a kungiyar NLC ya shaida a Abuja.

Ana sa ran kungiyoyin za su fitar da sanarwa jim kadan kafin a fara tattaunawa da gwamnati.

Yajin aikin wanda ya fara a ranar Litinin an yi shi  ne domin nuna rashin amincewa da gazawar gwamnatin tarayya na amincewa da sabon mafi karancin albashin a ranar 31 ga watan Mayu da kuma gazawarta wajen sauya karin kudin wutar lantarki.

More from this stream

Recomended