Ƴan ƙungiyar IPOB sun kashe sojoji biyu a wani farmaki da suka kai kan wani shingen binciken ababen hawa dake umuopara a ƙaramar hukumar Abia south ta jihar Abia.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba bayan da wasu mahara da ba a san ko su waye ba suka farma sojojin dake binciken ababen hawa.
A cikin wata sanarwa ranar Laraba, Jonah Umuakhalu mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya shiya ta 82 ya ce ƴan ƙungiyar IPOB dake fafutukar kafa ƙasar Biafra su ne da alhakin kai harin.
Umuakhalu na magana ne da yawun rundunar tsaron haɗin gwiwa ta Operation UDO KA dake yankin kudu maso gabas ya ƙara da cewa jami’an tsaron sun samu nasarar daƙile harin kuma wasu daga cikin maharan sun tsere da raunin harbin bindiga.
Ya shawarci mazauna yankin da suke ƙwararan bayanan sirri da su bawa jami’an tsaro bayani kan maharan.