Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta buƙaci a koma sayar da fetur a tsohon farashin lokacin Buhari

Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta koma sayar da mai a tsohon farashin kuɗin mai na watan Yunin shekarar 2023.

Kiran na TUC na zuwa ne biyo bayan ƙarin farashin kuɗin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi a baya bayannan.

Gabanin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya cire tallafin man fetur  a ranar 29 ga  watan Mayu  2023 ana sayar da kowace litar mai kan kuɗi daga ₦195 ya zuwa 238 a sassa daban-daban na Najeriya..

Amma ƙarin da aka yi na kwanakin nan ya sa farashin litar mai ya koma ₦998 a Lagos da kuma 1,003 a Abuja.

Ƙungiyar masu gidajen mai ta danganta ƙarin kuɗin man fetur da ƙalubalen da ake fuskanta wajen shigo da man.

A wurin wani taron manema labarai a ranar Alhamis, shugaban ƙungiyar TUC, Festus Osifo ya shawarci gwamnati da ta saka hannu a lamarin ta hanyar samar da dalar Amurka mai sauƙi ga matatar man fetur ta Dangote.

“Muna son farashin man fetur ya koma ƙasa da yadda yake a baya ba wai kawai ya koma yadda yake a da ba a’a ƙasa da haka,” ya ce.

Ya jaddada muhimmancin buƙatar gwamnati da ta  bawa matatar Dangote canjin kuɗin ƙasashen waje akan ₦1000/$1  mai makon ₦1600 da ake sayar da dala ɗaya a yanzu.

More from this stream

Recomended