Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice daga taron.
Gwamnatin ta kira taron ne domin tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashi da za a riƙa biyan ma’aikata a Najeriya.
Joe Ajaero shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC da kuma Tommy Okon mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadago ta TUC sune suka wakilci ma’aikata a wurin taron.
Da yake magana da ƴan jaridu a wurin taron Ajaero ya yi allah wadai da tayin biyan ₦48,000 da gwamnatin tarayya ta yi a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Ya ce gwamnatin ba da gaske take ba kan tattaunawa da take da ƴan kungiyar ƙwadagon.
Ajaero ya ce gwamnati na da kwanaki har zuwa ƙarshen wannan watan domin ta fitar da matsayarta kan batun.
Tun da farko ƙungiyoyin TUC Da NLC sun miƙawa gwamnati buƙatar ta riƙa biyan ₦615,500 a matsayin mafi ƙarancin albashi.