Alhaji Wosai wani mamba a ƙungiyar ƴan ta’addar Boko Haram ya miƙa kansa ga dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai.
Rahotanni sun bayyana cewa ɗan ta’addar ya miƙa kansa ga dakarun 21 Amored Brigade bayan da ya gudo daga sansanin mayaƙan na ƙungiyar Boko Haram dake ƙauyen Garno a jihar Borno.
Wasu majiyoyin jami’an tsaron sirri sun faɗawa Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi cewa ɗan ta’addar ya miƙawa sojoji bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya gidan zuba harsashi guda ɗaya dake ɗauke da harsashi 39.
Ana cigaba da samun ƴan ta’addar Boko Haram dake miƙa kansu ga jami’an tsaro biyo baya matsin lamba ta hanyar farmaki da dakarun sojan Najeriya suke cigaba da yi musu.