Wani ɗalibi da ya kammala Jami’ar Ambrose Ali(AAU) dake Ekpoma a jihar Edo ya yi yunkurin hallaka kansa bayan da ya zargi jami’ar da kin bashi takarardar sakamakon kammala karatu.
Ɗalibin mai suna Precious Ogbeide ya kammala karatu a Jami’ar a shekarar 2018 amma ya koka cewa ba a bashi takarardar kammala karatu ba.
Jaridar Punch ta rawaito cewa iyayen Ogbeide sun bayyana cewa ya dadde yana fama da matsananciyar damuwa saboda rashin karbar shedar kammala jami’ar bayan da ya shafe shekaru biyar yana karatu.
Ɗalibin ya rika kekketa jikinsa da guntun fasasshiyar kwalba.
Suma wasu tsofaffin daliban jami’ar sun koka kan yadda har yanzu jami’ar ta gaza basu shedar kammala karatu.