Ɗalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin wutar lantarki a wuraren kwanansu.

Daliban sun kulle kofar makarantar, suna rera wakokin hadin kai tare da nuna kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban kamar, ‘Babu hasken da za a jika Garri’ da “Ba mu da SUG” yayin da wasu kuma suka rike bokitin da babu ruwa a ciki domin nuna rashin ruwa a makarantar. 

Daliban sun koka da yadda lamarin ya janyo musu wahalhalu da kuma illa ga ayyukansu na neman ilimi.

Haka kuma an kulle da yawa daga cikin ma’aikata da shugabannin jami’ar a wajen kofar makarantar, inda aka hana su shigowa.

Sai dai babban jami’in kula da harkokin dalibai na Jami’ar, Farfesa Christopher Piwuna, ya tabbatar da kalubalen karancin ruwa da kuma katsewar wutar lantarki a gidajen daliban.

Ya kuma ɗora alhakin lamarin a kan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Jos a kan wani bashin da yake bi.

More News

Zanga-zanga: An jibge ƴan sanda 4200 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haƙuri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...