Ɗalaibai 200 gini ya ruguzo kansu a Jos

Ɗalibai kusan 200 ne suka maƙale cikin ɓaraguzan ginin makarantar da ya rufta da safiyar ranar Juma’a a garin Jos a cewar kwamishinan yaɗa labarai na jihar Filato, Mr Musa Ashoms.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa ginin makarantar sakandaren Saint Academy a Jos ya rufta ranar Juma’a lokacin da ɗalibai suke rubuta jarabawar ƙarshen zangon karatu na uku.

Ashoms wanda ya ziyarci wurin tare da rakiyar wasu kwamishinoni ciki har da na ilimin sakandare ya ce makarantar na da jumullar ɗalibai 400.

Kwamishinan ya ce ɓangaren ginin makarantar da ya rufta na ɗauke da dalibai 200.

Ya ce ruftawar ginin ya jawo asarar rayuka kuma har yanzu ana cigaba da kai waɗanda suka jikkata ya zuwa asibiti saboda haka baza a iya tabbatar da yawan mutanen da lamarin ya shafa ba har sai an kammala zaƙulo kowa dake ciki.

Ya ƙara da cewa tuni gwamnan, Caleb Mutfwang  jihar ya umarci ma’aikatan lafiya da su tabbatar sun ceto rayuka waɗanda aka zaƙulo daga ɓaraguzan ginin makarantar.

More from this stream

Recomended