Ƴansandan sun yi artabu da ƴanbindiga a Abuja

Jami’an ‘yan sanda daga babban birnin tarayya Abuja sun kashe wani dan bindiga tare da cafke uku a wani samame da suka kai.

Ƴan sandan sun kai samamen ne a wata maboyar masu garkuwa da mutane a garin Chikara da ke kan iyaka da jihar Kogi.

Duk da haka, wannan ya haifar ba-ta-kashi tsakaninsu da ƴansandan.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar Asabar ta hannun mai magana da yawunta a Abuja, Josephine Adeh, ta bayyana wadanda ake zargin a matsayin Mahammadu Isa, Likita Idris, da Isiyaku Muhammedu. 

More from this stream

Recomended