Ƴanbindiga sun kashe mataimakin shugaban jami’ar UDUS


Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe mataimakin shugaban jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Yusuf Sa’idu.

Jami’ar wadda ta bayyana rasuwar Saidu a wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Litinin, ta ce ‘yan ta’adda sun kai wa marigayin hari tare da kashe shi a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga jihar Sakkwato. 

Sanarwar ta ce, “Farfesa Yusuf Sa’idu, mataimakin shugaban jami’ar bincike da ci gaba na Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto ya rasu a halin yanzu. 

“’Yan bindiga sun kai masa hari tare da kashe shi a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Jihar Sakkwato.”

More from this stream

Recomended