Ƴanbindiga sun ƙwace makamai daga hannun sojojin Najeriya

Wani faifayin bidiyo ya bayyana a yanar gizo wanda ke nuna yadda madugun ‘yan fashi, Bello Turji da ’yan tawagarsa suke murnar karbe makamai daga hannun sojojin Najeriya. 

Turji da yaransa sun kuma karbe harsashi da dama daga hannun sojojin na Najeriya a lokacin da suka kama manyan motocin yaƙin.

Wani kwararre kan harkokin tsaro da yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, ZagaZola Makama ya tabbatar da hakan. 

Makama ya ce an samu rahoton tashin hankali daga rundunar da ke nuni da wani babban taron ‘yan bindiga a wani wurin da aka kebe a sansanin Bello Turji.

Daga nan aka tura tawagar sojoji cikin gaggawa zuwa yankin, wanda wani matashin jami’i ya jagoranta amma motar tawagar ta makale a cikin wani wuri mai dausayi, wanda ya hana su ci gaba da afkawa ƴanbindigar.

Makama ya bayyana cewa, sojojin sun fuskanci munanar turjiya daga ‘yan bindigar.

Yankin Arewa maso Yamma dai yana ta fama da ta’addancin ƴanbindiga.

More from this stream

Recomended