A ranar Talata 25 ga watan Yuni wasu ƴan ta’adda sun kai harin kwanton ɓauna a Tassia Sun Badjo a jihar Tillaberi dake Jamhuriyar Nijar inda suka kashe sojoji 21 tare da jikkata wasu 9.
Munin da harin ya yi ya sa gwamnatin ƙasar ta Nijar ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki domin girmama dakarun sojan da suka mutu.
Harin ya faru ne akan iyakar Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso da Mali yankin dake fuskantar yawan hare-hare daga ƴan ta’adda dake biyayya ga ƙungiyar Al’qaida.
Rikicin na ƴan ta’adda dake cigaba da gudana a yankin Sahel ya jawo asarar duban rayuka tare da raba wasu miliyoyin mutane da muhallinsu.
Harin na zuwa ne a yayin da gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta Nijar da ta ƙwace mulki a shekarar da ta wuce ke cigaba da fuskantar matsin lamba daga maƙotan ƙasashe kan tawo ƙarshen hare-haren da ƴan ta’addan suke kai wa.