Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tangaza/gudu ta jihar Sokoto a majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Sani Yakubu ya ce ‘yan bindiga daga Nijar da Mali da Libya da takwarorinsu na kananan hukumomin Tangaza na jihar sun sanya haraji kan manoma.
Yakubu, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da kudiri a zauren majalisar a ranar Larabar da ta gabata, ya ce mazabar Tangaza/Gudu na kewaye da dazuzzuka biyu; Dajin Tsauna wanda ya ratsa zuwa Gwadabawa, Illela da Jamhuriyar Nijar da dajin Kuyan Bana wanda ya kai Gudu da Jamhuriyar Nijar.
Dan majalisar ya ce ‘yan ta’addan da ke yin sintiri a wurin sun hada karfi da karfe, lamarin da ya sa jami’an tsaron da aka tura ke da wuya su magance matsalar rashin tsaro a yankin baki daya.
Yakubu ya kara da cewa, duba da yadda al’ummar yankin galibi manoma ne, ‘yan fashin sun sha alwashin dakatar da ayyukan noman na bana idan al’ummomin suka ki biyan harajin da aka dora musu.