Ƴan Sudan sun yi raddi kan sauya dokokin kasarsu

Bikin zagayowar ranar da aka fara bore a birnin Atbara na Sudan

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Bayan shekara 30 na mulkin Islama, gwamnatin Sudan ta kafa sabbin dokoki da za su ba ƴan kasar wadanda ba Musulmi ne ba damar shan barasa, baya ga soke dokar hukunta wadanda suka yi ridda.

A makon jiya aka kaddamar da wasu sabbin dokoki, amma wannan ne karon farko da hukumomi ke bayyana abin da suka kunsa.

Ministan Shari’a na Sudan Nasredeen Abdulbari: “Za mu yi watsi da dukkan dokokin da ke take hakkin bil Adama a Sudan.”

Akwai kuma wata sabuwar doka da ta haramta yi wa mata kaciya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A farkon watan Mayu Sudan ta kafa dokar hana yi wa mata kaciya

A karkashin dokokin, mata na da ikon yin tafiya zuwa ko’ina tare da ƴaƴansu ba sai sun nemi izini daga wani ɗan uwansu namiji ba.

Wasu Musulmi ƴan Sudan na mayar da martani da ke nuna rashin jin daɗinsu ga wannan matakin

Matakin bai yi wa al’umar Musulmin kasar daɗi ba

Hussaini Bashir Ahmad ɗan jarida ne da ke aiki a tashar Radio Africa da ke Khartoum, kuma mai bibiyar siyasar kasar ne.

Ya ce da alama matakin bai yi wa al’umar Musulmin kasar daɗi ba:

“Duk da sakaci na ƴan Sudan, da kuma yadda suke son walwala da ƴanci, waɗannan sabbin dokokin ba su yi mu su daɗi ba.”

Ya kuma ce wasu ƴan kasar sun fara kokawa da matakin tun kafin a fara aiwatar da shi, “Suna cewa tafarkin dimokraɗiyya ya zama mu su masifa, ya zama mu su bala’i.”

Ba kowa ne ke kokawa ba

Akwai ƴan Sudan da dama da ke bin addinin Kirista, akwai kuma waɗanda ma ba ke bin addinai na gargajiya, sai dai asalinsu daga Sudan ta Kudu suke, lamarin da ya sa suka ci gaba da bin addinin kakaninsu duk da cewa suna zaune ne a kasar da Musulmai suka fi yawa.

Akuei Deeg mai bin addinin Kirista ne kuma mazaunin Bahry ne a tsakiyar birnin Khartoum, wanda yankin kasuwaci ne da manyan otel-otel.

Ya ce duk da cewa shan barasa ba laifi ne a addini da yake bi ba, amma ba ya iya shan giya tun da ko a otel-otel da ke birnin ba sa sayar da ita.

Ya kuma ce mabiya addinin Kirista har ma da mabiya addinan gargajiya sun ji dadin kafa dokar da ta ba su damar shan barasa:

“A shekarun baya, ba wanda ya isa ya sha barasa a a bainar jama’a.”

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A boye ake hada barasa da shan ta a Sudan

A cewarsa a boye suke haɗa giya domin gudun fushin hukuma, “Mu kan yi barasarmu a cikin gida ne, kuma mu kan shanye ta a cikin gidajenmu ne.”

Tun bayan da aka hambarar da Omar al-Bashir daga karagar mulki, sabuwar gwamnatin kasar karkashin firai minista Abdallah Hamdok ta sha alwashn mayar da kasar bisa tafarkin dimokraɗiyya.

Sai dai kokarin na ta ya ci karo da bukatun yawancin ƴan kasar wadanda Musulmi ne.

‘Ba mu amince ba’ – kungiyoyin matasa

Amma wasu daga cikin kungiyoyin da suka yi fafutkuar hambarar da gwamnatin, kuma suka yi tsayin-daka hara aka kafa wannan gwamnatin sun fara kokawa.

Al-Sari Hassan shi ne sakataren kungiyar “Sudan Professionals Association” a Omdurman, kuma yana cikin matasan da suka shafe watanni suna zanga-zanga har sai da aka hambare tsohon shugaban kasar a bara:

“Munafuncin da kulle-kullen da magoya bayan tsohuwar gwamnati ke yi na lalata saauyin da muka sadaukar da rayukanmu wajen kafawa.”

“Mun haɗa kanmu ne domin ƙwato kasarmu daga hannun azzalumai, amma sai ga shi wasu na neman rusa tafarkin da aka gina kasarmu,” inji shi.

Ya kuma ce, “Za mu ci gaba da gwagwarmaya har sai komai ya daidaita a Sudan. Ba mu amince da wadannan matakan ba, kuma ba da goyon bayanmu ake yin wadannan sauye-sauyen ba.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sudan dai ta daɗe cikin rikici: Daga na Darfur zuwa na Kordofan a kudancin kasar, da kuma na tsakaninta da Sudan ta Kudu kan mallakar Abyei

Waɗannan dokokin da sauye-sauyen na zuwa ne bayan an hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a bara bayan ya shafe shekara kusan 30 yana mulkin kasar.

Me malaman addinin Musulunci ke cewa?

Amma har yanzu ba a ji daga bakin malaman addinin Musuluncin kasar kamar su Sheikh AbdulHayy Yusuf ba.

Malumman addinin Islama na da karfin fada aji a ciki da wajen kasar.

Osman Faroug Adam Musulmi ne, kuma kamar yawancin Musulmin kasar, yana biyayya ga dukkan umarnin da malamansa irin su Sheikh AbdulHayy suka bayar.

A ganinsa kasar na iya fadawa cikin wani sabon rikici na idan ba a iya kashe wannan wutar da ke ruruwa ba.

“Sudan kasar akasarin Musulmai ce, kuma babu yadda za mu kyale ta koma karkashin ikon tsirarrun mutanen da ba su damu da addininmu da makomarmu ba.”

Sudan dai ta daɗe cikin rikici – tun daga na yankin Darfur a yammacin kasar zuwa na Kordofan a kudanci, da kuma wanda ke tsakaninta da Sudan ta Kudu kan wanda ya mallaki yankin Abyei mai arzikin man fetur.

More News

Peter Obi Ya Ziyarci Mutanen Da Su Ka Ƙone Sakamakon Wutar Da Wani Ya Cinnawa   Masallaci A Kano

Ɗan takarar shugaban ƙasa  a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam'iyar Labour Party (LP) Peter Obi ya ziyarci mutanen da wani matashi ya cinnawa wuta a...

An sanar da zaman makoki na kwana biyar saboda mutuwar shugaban kasa a Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi...

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...